Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ila yau ya taya alummar kasar murnar kafa sabuwar gwamnati kuma ya jaddada cewa kasar Iran ba za ta nuna gazawa ba wajen ci gaba da taimakawa kasar ta Labanon idan bukatar hakan ta taso.
Amir Abdullahiyan ya kara da cewa Iran ta yi amanna cewa kasar Labanon za ta shawo kan matsalolin da take fuskanta ba tare da ba ta lokaci ba ,
Ana sa ran ministan harkokin wajen na kasar Iran zai gana da shugaban kasar Labanon Micheal Aun da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Birri, da kuma fira manistan kasar Najib Mikati ka na da takwaransa na kasar Abdullah Bob Habin, daga karshe kuma ya gana da wakilin kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinu a ofishin jakadancin Iran dake Berut.
342/